Dakarun sojin Najeriya sun kwato Bindigu 44 daga hannun wasu yan ta'adda 3

Share:

Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da da kama wasu mutane uku (3) da ake zargin yan ta'addane a yayin da suke safarar Bindigu zuwa kauyen Bena dake cikn karamar hukumar Wasagu ta hijar Kebbi, kauyen dake da iyaka da jahar Zamfara.

mataimakin kakakin rundunar ta daya na rundunar sojin Najeriya, kanal Muhammad Dole ne ya sanar da haka ranar Laraba 12 ga watan Disamba, inda yace sojojin sun kama yan ta'addan ne a ranar Talata 11 ga watan Disamba, a yayin binciken ababen hawa a garin Rijau na jahar Neja.

            Kanal dole ya bayyana sunayen yan ta'addan kamar haka ; Shehu Samai'la dan shekara 25, Aminu Umar dan shekara 32 da kuma Bilyaminu Abdullahi dan shekara 22, inda ya bayyana sun kamayan ta'addan ne dauke da Bindigu guda arba'in da hudu (44).

Bugu da qari kakakin yace sun kwato kwankunan harsashi guda dari uku da hamsin da daya (351), duk a cikin motar da yan ta'addan ke ciki mai dauke da lambar rijista  ZUR DX28 Kebbi, yayin da suke kan hanyarsu ta shiga jahar Kebbi.

"Bincikenmu  ya gano cewa yan bindigan na kan hanyarsu ta zuwa kauyen Bena ne dake cikin karamar hukumar Wasagu dake jihar Kebbi, wan kuma yana da iyaka da jihar Zamfara.

Wannan kamen da muka yi yazo daya da wani mutumi, Rabiu Akilu da muka kama dauke da bindigu  36 da Alburusai 343 a cikin motar sa yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa zamfara a watan Nuwanba." inji shi.

Daga karshe Kanal yace dole zasu cigaba da gudanar da bincike akan Aminu, Shehu da Bilyaminu domin jin wanda  zasu kai ma makaman da kuma wanda ya basu makaman, don haka yayi kira ga Direbobi da su taimaka ma sojoji da sahihan bayanai game da ayyukan yan bidiga.

Kanal Dole ya bayyana sunayen yan ta’addan kamar haka; Aminu Umar dan shekara 32, Shehu Samaila dan shekara 25 da kuma Bilyaminu Abdullahi mai shekaru 22, inda ya kara da cewa sun kama yan ta’addan dauke da bindigu guda arba’in da hudu (44). Haka zalika kaakakin yace sun kwato kwankunan alburusai guda dari uku da hamsin da daya, 351, duk a cikin motar da yan ta’addan suke ciki mai lamban rajista ZUR 28DX Kebbi, yayin da suke kan hanyarsu ta shiga jahar Kebbi. “Bincikenmu ya binciko yan bindigan na kan hanyarsu ta zuwa kauyen Bena ne dake cikin karamar hukumar Wasagu na jahar Kebbi, wanda kuma yana da iyaka da jahar Zamfara. "Wannan kamen da muka yi yazo daya da wani mutumi, Rabiu Akilu da muka kama dauke da bindigu 36 da alburusai 343 a cikin motarsa yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Zamfara a watan Nuwamba.” Inji shi. Daga karshe kanal Dole yace zasu cigaba da gudanar da bincike akan Aminu, Shehu da Bilyaminu domin jin wanda zasu kai ma makaman da kuma wanda ya basu makaman, don haka yayi kira ga direbobi dasu taimaka ma Sojoji da sahihan bayanai game da ayyukan yan bindiga. Read more: https://hausa.legit.ng/1209166-rundunar-sojojin-najeriya-sun-kama-yan-taadda-3-sun-kwace-bindigu-44.html?fbclid=IwAR3MDpvc0Y1ubbWGO5EUxV_NBRm8Z7s6zcy4wbNw16BNd-gDY7KquRuKOJI

No comments